Jama’a Sun Ƙauracewa Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Kano Yayin da aka Hango Yara Ƙanana na Zaɓe a Wasu Wuraren

0
221

 

Zagayen da jaridar PRIME TIME NEWS ta yi ya nuna al’ummar jihar Kano da dama sun kauracewa zaben kananan hukumomi dake gudana a jihar Kano inda kalilan ne suka fito.

Baya ga matsalolin rashin isar kayan aiki da ma’aikatan zabe zuwa rumfunan zabe, rahotanni sun bayyana cewa, iya wakilan jam’iyyar APC kadai ake gani a wajen zaben.

An gano wakilin jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomi dake gudana a Kano na fadawa wani mutum da ya dangwala jam’iyyar fiye da sau daya kamar yadda jaridar Politics Digest ta rawaito.

Hakan na daga cikin abinda ya sabawa dokar hukumar zabe ta jihar Kano.

Wani mai sanya ido ya shaidawa Politics digest cewa, “Al’umma basu da kwarin gwiwa kan yadda zaben ke gudana, babu yan hamayya yayin da wakilan jam’iyya ke zabar jam’iyyar da kansu”.

Sannan kuma a wasu wuraren rahotanni sun bayyana cewa, kananan yara wadanda shekarunsa bai kai ba ne suka dinga kada kuri’a.

Sai dai Hukumar Zabe ta jihar Kano wato KANSIEC ta musanta batun na cewa yara suna yin zabe, yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban hukumar ya ce an baiwa jami’an tsaro umarnin kama duk yaron da aka samu yana zabe.

Idan za’a iya tunawa dai, Jam’iyyar PDP a jihar wacce ita ce babbar mai hamayya ta bayyana cewa baza ta shiga zaben ba inda ta yi zargin cewa baza ayi mata adalci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here