Fina-Finai Da Jaruman Da Suka Lashe Kambun Karramawar Kannywood a 2020

0
395
Usman Solo

Daga Musa Sani Aliyu

Kallo irin na tsanaki, kallo da ido na basira, duba da ido irin na dubarudu, kallo da ido na hange daga nisan dake tagar tazarar tazar tsifar tsefe tsarin Fina Finai baiwa ce kuma ilimi ne mai zurfi.

Usman solo guda daga cikin masu sharhi akan Fina Finai, al’amuran yau da kullum da tsokaci kan Finai Finan hausa, Indiya, da sauran al’amuran kirkira na duniya baki daya, ya fitar da Jadawalin dake nuni da kambun bajintar da wasu zababbun Fina Finai da Jarumai, da masu bada umarni, harma da wakoki na shekarar 2020 da ta shude da sukai carar zakaran gwajin dafin lashe lambobin yabo da karramawa, bisa layin su a tsari tsab.
Usman Solo ya lakabawa wannan salo mai jan zaren allon zuciya da hankali da ” KANNYWOOD TOPPERS 2020″.

A cikin jerin jumullar jadawalin da zaizo a kasa, Usman Solo ya fitar da reshina na Jaruman Jarumai, Sababbin fuskoki da sauransu. Usman Solo ya duba turaku dayawa,da bangarori da dama kana ya waiwayi sinadarai masu dumbin yawa bisa mizani,kazalika ya auna a awon mizanin kwanon awon daya dace na rassa sama da goma,sannan yai ninkaya a tafkin tsammo wannan Jadawali kamar haka:

FIM MAFI CINIKI- (Mati A Zazzau)

FITACCEN FIM- (Bana Bakwai)

FITACCEN DARAKTA_ Ali Nuhu ( Bana Bakwai)

JARUMIN JARUMAI- Saddiq Sani Saddiq ( Mati A Zazzau)

JARUMAR JARUMAI- Maryam Yahaya ( Gidan Kashe Ahu)

FITACCEN MAI TAIMAKAWA JARUMI_ Saddiq Sani Saddiq ( Bana Bakwai)

FITACCIYAR MAI TAIMAKAWA JARUMA- Bilkisu Abdullahi (Bana Bakwai) da kuma Amal Umar ( Gidan Kashe Ahu)

FITACCEN FIM MAFI KAYATARWA_ Mati A Zazzau

FITACCIYAR WAKA_ Jaruma Kina Lokaci (Jaruma) Abdul D, One da Murja Baba.

FITACCEN MAWAKI- Abdul D One ( Ba Sabo- Fati)

FITACCIYAR MAWAKIYA_ Murja Baba( Jaruma Kina Lokaci- Jaruma)

FITACCEN FIM MAI DOGON ZANGO_ ( Labarina )

FITACCEN DARAKTA( FIM MAI DOGON ZANGO)_ Aminu Saira ( Labarina)

JARUMIN JARUMAI( FIM MAI NISAN ZANGO)_ Lawan Ahmad ( Izzar So)

JARUMAR JARUMAI (FIM MAI NISAN ZANGO)_ Nafisa Abdullahi ( Labarina)

FITACCEN SABUWAR FUSKA_ Yusuf Saseen ( Labarina)

FITACCIYAR SABUWAR FUSKA_ Aisha Najmu ( Izzar So) da Hajjo Adam ( Karamin Sani).

FITACCEN FIM MAFI KAYATARWA ( DOGON ZANGO)- Gidan Badamasi.

FITACCEN JARUMIN BAN DARIYA- Nura Dan Dolo ( Gidan Badamasi)

FITACCIYAR WAKAR DA BATA FIM BA- Jarumar Mata ( Hamisu Breaker) da “Zo Mu Sasanta” ( Salim Smart, Khairat, Murja Baba).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here