Budurwa Ta Rabu da Saurayinta a Kano Bayan ya Shiga Kungiyar Samari ‘Marowata’

0
257

Wasu masoya wadanda suka shafe shekaru 4 suna soyayya a Kano sun kawo karshen soyayyarsu sa’o’i kadan bayan Saurayin ya sanar a shafinsa na Facebook cewa ya shiga kungiyar Samari Marowata na Najeriya(SMAN).

Saurayin mai suna Muzamil, wanda ya sanar da shigarsa kungiyar a safiyar yau Juma’a, masoyiyar tayi blocking din sa a shafin Facebook.

Muazzamil ya shaidawa jaridar Sahelian Times a wata tattaunawa cewa da farko dai abun ya fara a wasa ne yayin da ta kira shi take fada masa cewa, ba dai-dai bane ya shiga kungiyar samari marowata.

Budurwar wacce bata so a bayyana sunanta ta tabbatarwa da jaridar Sahelian Times cewa baza ta ci gaba da soyayya da mutumin da ya shiga kungiyar da manufofinta ya sabawa addinin muslunci.

“Addinin musulunci ya hana rowa. ANNABI S.A.W ya ce duk marowaci bazai shiga Aljanna ba” inji ta yayin da take kare matsayinta na barin soyayyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here