Sarkin Karaye Ya naɗa Ƙanin Kwankwaso Sarautar Makaman Karaye

0
213

Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya nada Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso(Baba) a matsayin Makaman Karaye hakimin Madobi.

Kuma ya zama dan majalisar Sarki kana daya daga cikin masu zabar Sarki.

An amince da nadin ne a taron farko na wannan shekarar na masarautar Karaye da ya gudana jiya Laraba.

Taron masarautar ya yabawa Sarkin bisa girmamawa ga iyalan marigayi Makaman Karaye.

Yayin da yake taya murna ga sabon Makaman, ya bukace shi da ya dora daga inda mahaifinsa ya tsaya.

Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso wanda kani ne ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya gaji mahaifinsa wanda Allah ya yiwa rasuwa a kwanakin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here