Mallam Falalu Bello Mu ka Sani a Matsayin Shugaban PRP na Kasa – INEC

0
285

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa(INEC) a yau Alhamis ta yi bayanin cewa, ba ta san wani mai suna Sule Bello wanda ya yi ikirarin shugabantar jam’iyyar PRP na kasa ba.

Yayin da aka tuntubi hukumar zaben kan shin ta san da wani mai suna Sule Bello wanda ke ikirarin shi ne shugaban jam’iyyar PRP na kasa, hukumar zaben ta ce bata son da mutumin ba.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, mutumin da ta sani a matsayin shugaban jam”iyyar PRP na kasa shi ne Mallam Falalu Bello, OFR.

Hukumar ta ce sun tattauna da Mallam Falalu Bello da sauran shugabannin jam’iyyu kwanakin da suka wuce kan yin nazarin yadda zaben 2019 ya kasance da kuma tabbatar da nasarar yadda zaben shekarar 2023 zai kasance.

Hukumar ta kara da cewa, yakamata al’umma su ki amincewa da duk wanda ke kiran kansa a matsayin shugaban jam’iyyar indai ba Mallam Bello Falalu bane.

INEC ta kuma shawarci al’umma da su dinga ziyartar shafinta don sanin shugabannin jam’iyyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here