Ganduje Ya Bada Umarnin yin Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi ga Dukkan Mukarraban Gwamnatinsa

0
90

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni ga dukkan masu rike da mukamai a gwamnatinsa da suje ayi musu gwajin shan miyagun kwayoyi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ke yi.

Babban hadimi ga mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege, Mujahid Zaitawa ne ya bayyana hakan bayan ziyarar da ya kaiwa gwamnan sannan ya yabawa gwammnan bisa kokarin dakatar da masu shan kwaya daga yin takara a zaben kananan hukumomi.

A wata tattaunawa da Mujahid Zaitawa yayi da jaridar Sahelian Times ya ce, “an fara tantancewar a hukumar KAROTA Kuma za’a ci gaba a dukkan ofisoshin ma’aikatan gwamnati da kuma mukarabban gwamnati”.

Ya kara da cewa, ” zamu tabbata duk wanda aka samu da shan miyagun kwayoyi ya ajiye aiki”.

“Wannan abu ne da zai je har matakin tarayya, muna fatan a shekarar 2023, dukkan yan takara za’a yi musu gwajin shan miyagun kwayoyi ciki har da masu neman takarar shugaban kasa”, inji shi.

Sannan ya godewa Gwamnan na Kano tare da yin kira ga sauran gwamnoni su yi koyi da irin wannan manufar tare da aiwatar da ita a jihohinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here