Ganduje Ya aika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwar Auduwa Maitangaran

0
307

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya aika sakon ta’aziyyar rasuwar shugaban kungiyar yan kwangila ta jihar Kano, Alhaji Auduwa Maitangaran.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya bayyana Alhaji Auduwa Maitangaran a matsayin mutumin da ya jagoranci al’ummarsa bisa gaskiya da rikon amana.

“Shugaba ne shi da ya jagoranci mutanensa da Adalci, Amana, da Kyakkywar Alaka. Ya jagoranci kungiyar yan kwangila yan asalin jihar Kano, da son aiki.”

“Gwamnan ya ce rasuwar ba wai iya iyalan mamacin ta shafa ba, ” rashi ne da muka yi gabadaya. ta shafemu gabadaya.
Abinda ya rage garemu yanzu shi ne mu ci gaba da yi masa addu’a da rokon Allah ya yi masa Rahma ya gafarta laifukansa”, inji shi.

“Amadadin gwamnatin jihar Kano da al’ummar Kano, ni Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan jihar Kano ina mika ta’aziyya ga iyalai, kungiyar yan kwangila ta jihar Kano, Abokansa da duk masu fatan Alkhairi. Allah ya yafe masa zunubansa yasa aljanna makomarsa” inji gwamnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here