Bidiyon wata Wakar Hausa dake Nuna Hotunan Tsiraici ya haifar da Ce-ce kuce a Shafukan Sadarwa

0
273

Wani Bidiyon wakar Hausa da aka sanya a shafin YouTube da sauran shafukan sadarwa sun haifar da ce-ce kuce da yin Allah-Wadai a yayin da wakar ke nuna hotunan tsiraici.

Bidiyon wakar mai suna ‘North Vibe’ wanda mawaki Abdullahi Aliyu Shelleang dan jihar Adamawa ya yi, inda kuma suka yi tare da Mawakin jihar Legas, SlimCase.

Jama’a da dama sun yi Alla-wadai da bidiyon wakar inda da dama suka bayyana cewa wakar ta saba da al’adun Hausa.

Wani mai suna Tajuddeen Musbahu ya bayyana ra’ayinsa kamar haka: “Wannan ya saba da al’adu da halayyar mutanen Arewa.

“Wannan cin fuska ne ga Hausawa, idan za’a dau shawarata zan ce a goge bidiyon. Hakan ba dai-dai ba ne”.

Wani ma ya rubuta “Ina da tabbacin wannan mutumin ba daga Arewa yake ba.

“Tayaya zai yi irin wanann a Hausa kuma ba wanda ya kula da shi.

“A zance na gaskiya, ba wani yare a Najeriya da zai so a alakanta shi da wannan Bidiyon.”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here