An Raba Tallafin Naira Dubu 10 Ga Masu Karamin Karfi Dubu 1 Garin Babura

0
107

An rabawa masu karamin karfi fiye da dubu daya naira dubu goma-goma kowannen su a karkashin shirin tallafawa masu karamin karfi na Gwamnatin tarayya a yankin Karamar Hukumar Babura.

Haka zalika kimanin mata dari biyar ne suka samu tallafin naira dubu ashirin- ashirin domin bunkasa kananan sana’oinsu a yankin.

Jami’in kula da shirin a karamar hukumar, Malam Ado Ya’u Jigawa ya bayyana haka lokacin raba tallafin a garin Babura.

Ya ce kimanin naira miliyan goma aka rabawa masu karafin karfi Maza da Mata domin su kasance masu dogaro da kansu.

Malam Ado Ya’u,  daga nan ya shawarci wadanda suka samu tallafin su yi cikakken amfani da shi domin cigaban rayuwar su.

Wasu daga cikin wadanda suka samu tallafin sun yabawa gwamnatin tarayya da ta jihar Jigawa bisa bullo da wannan shiri, tare da alkawarin yin amfani da kudaden wajen inganta rayuwar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here