An Kama wani Saurayi Bisa Zargin Yin Lalata da Yarinya Ƴar Shekara 5 a Unguwar Kofar Ruwa dake Kano

0
263

Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, reshen jihar Kano, ta kama wani Saurayi dan shekara 18, Mai suna Isma’eel Abubakar bisa zargin yin lalata da yar shekara 5.

Mai magana da yawun hukumar ta NSCDS, ASC Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau Laraba a Kano.

Ibrahim Abdullahi ya ce wanda ake zargin mazaunin unguwar Kofar Ruwa ne dake Kano, jami’an rundunar ne dai suka kama shi a ranar 8 ga watan Janairu bayan ya yaudari yarinyar zuwa dakinsa dake unguwar Kofar Ruwa a Kano tare da yin lalata da ita.

Ya kara da cewa, wanda ake zarin makoci ne na yarinyar, kuma ya amsa laifunsa.

“An kama bincike kan lamarin za kuma a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here