Za’a Koma Makarantu Ranar 18 ga Watan Janairu – Kwamitin Yaki da Korona

0
249

Kwamitin yaki da cutar Korona a yau Talata ya ce za’a koma makarantu a fadin kasarnan ranar 18 ga watan Janairu har zuwa lokacin da ma’aikatar ilimi za ta sanar da mataki na gaba.

Babban jami’in tsare-tsare na kwamitin, Dr. Sani Aliyu ne yayi bayanin hakan yayin wani shirin gidan Talabijin da aka yi yau.

Ministan ilimi, Adamu Adamu a jiya Litinin ya ce gwamnatin tarayya za ta sake yin nazari kan ranar 18 ga watan Janairu da aka sanya tunda farko don komawa makarantu.

Yayin da yake karin haske kan batun, Dr. Sani Aliyu ya ce, Ministan bai ce an sauya ranar komawa makarantu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here