Za mu Kara Sanya Dokar Kulle Matukar Yan Najeriya Su ka Ci gaba da Kin bin Matakan Kariya – Kwamitin Yaki da Korona

0
128

Kwamitin yaki da cutar Korona a yau Talata ya ce, halayyar yan Najeriya na bi ko kin bin ka’idojin kariya daga cutar Korona ne zai fayyace ko za’a kara sanya dokar kulle yayin da ake fama da annobar zagaye na biyu.

Babban jami’in tsare-tsare na kwamitin, Dr. Sani Aliyu ne yayi bayanin hakan yayin gabatar da wani shirin Talabijin.

Ya ce, har yanzu ba a yanke shawara kan kara sanya dokar kulle ba amma halayyar da al’umma ke nunawa zai fayyace yadda kwamitin zai sanya ko kin sanya dokar.

“Ba kwamitin yaki da Korona ne zai yanke shawarar sake sanya dokar kulle ba, sai dai halayayyar da al’umma ke nunawa kan dokokin kariya daga cutar ne zai sa a kara sa wa. Akwai kasashen ketare da suke daukar matakan kariya kuma kowa na bin matakan. Jirage na zuwa, makarantu suna bude, guraren bauta na bude kuma basu da matsalar Korona saboda kowa na bin matakan kariya.

“Gaskiya ba ma son shiga dokar kulle saboda bama son kara kulle mutane, muna bukatar mu yi duk abinda za mu iya wajen kare kanmu daga kaiwa wajen da gwamnati za ta dau mataki”.

Idan za’a iya tunawa dai, a watan Maris na shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta sanya dokar kulle ta mako 5 a jihohin Legas, Ogun da birnin tarayya Abuja don dakile yaduwar cutar Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here