PDP ta sha Alwashin cinye zaben Kananan hukomomi na jahar Kano – Bako Lamido

0
475

 

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Shugaban Jam’iyyar PDP, reshen jahar Kano, tsagin jagorancin Ambassada Aminu Wali, da sanata bello Hayatu Gwarzo, sun sha Alwashin samun nasara a zaben Kananan hukumomin jahar Kano da za’a Gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Da yake Gudanarda jawabi A yau Litinin wajen bikin rabawa Yan takarar Jam’iyyar PDP, a shiyyar arewacin Kano, Alh. Mahmina Bako lamido yace jama’ar nijeriya sun gaji da mulkin Kama karya na APC saboda haka Yan takarar jamiyyar PDP, susha kuruminsu domin sune zasu lashe zaben da za’a gudanar na Kananan hukumomi a jahar kano,.

Bikin Rabawa Yan Takarkarin ta na Arewacin Kano, Tutar Takara yasamu halartat jiga jigan jam’iyyar a jahar Kano,.

A Jawabinsa Alh. Yahaya Bagobiri Wanda ya Wakilci Jagororin Jam’iyyar Ambassada Aminu Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo yayi kira ga daukacin ‘Ya ‘Yan Jamiyya dasu Tabbatar Sun zabi PDP, kuma sun Jajirce Sun Kafa Sun tsare Sun Tabbatar da Zaben da Sukayi.

An rabawa Daukacin Yan takarkarin Jam’iyyar da matemakansu Tuta da suka fito daga Kananan hukumomi 13 na Kano Ta Arewa A Garin Bichi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here