Hukumar Tsaro Ta DSS ta Bankaɗo Shirin Tayar da Rikicin Addini a Wasu Jihohin Najeriya

0
316

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bankado shirin haifar da rikicin addini a wasu jihohin Najeriya.

Hukumar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwar da kakakin hukumar na kasa, Peter Afunanya ya fitar yau Litinin a Abuja.

“Hukumar tsaron farin kaya ta DSS na sanar da al’umma kan shirin da wasu ke yi Wadanda ke aiki da wasu daga wajen kasarnan don haifar da rikicin addini a fadin kasarnan.

“Jihohin da suke hako sun hada da Sokoto, Kano Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos da wasu a yankin kudu maso gabas”.

Hukumar ta yi bayanin cewa ana shirin amfani da yan ta’adda wajen kai hari wuraren bauta da wasu muhimman mutane.

“Wani bangare na shirin shi ne na haifar da rikici tsakanin addinai da kuma amfani da masu tada zaune tsaye wajen kai hari wuraren bauta, shuagabannin addinai, manyan mutane da wuraren haduwar mutane.”

Sannanan hukumar ta shawarci yan Najeriya da su kaucewa duk wani abu da zai kawo rabuwar kai ko wanda zai haifar da rikici tsakaninsu.

Haka kuma hukumar ta ce zata ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya haka kuma ta gargadi masu wannan shirin da su dakatar da shi don zaman lafiya da kuma ci gaban kasa.

“Haka kuma, ana kira ga yan kasa da su mika duk wani rahoto kan abinda basu yarda dashi ba ga hukumomin tsaro dake kusa da su”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here