Hadimin Ganduje Ya Kalubalanci Abdullahi Abbas Kan Yaje ayi masa Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi

0
206

Hadimin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kalubalanci shugaban riko na jam’iyyar APC da yaje ayi masa gwajin shan miyagun kwayoyi.

Injiya Mu’az Magaji ya yi zargin cewa, yan takarar da shugaban jam’iyyar APC din ya sanya a kananan hukumomi an same su da ta’ammali da miyagun kwayoyi bayan gwajin da hukumar NDLEA ta yi musu.

Mu’azu Magaji ya ce “An yi min gwaji, kuma na tsallake; mun gode Allah, amma a yau yaran da ka kakaba a matsayin yan takarar shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli an tabbatar da suna shan kwayoyi”, inji shi.

Injiniya Magaji ya kara da cewa, ” Yanzu abinda ya rage shi ne kaje kaima ayima gwajin, duk da mun san yadda sakamakon gwajin zai kasance”.

Alaka dai ta yi tsami tsakanin Mu’azu Magaji da Abdullahi Abbas yayin da kowa ke caccakar juna.

An hango shugaban rikon na jam’iyyar APC na gugar zana ga Mu’azu Magaji a wani faifan Bidiyo a gaban gwamnan jihar ta Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here