An Soki Ahmed Musa Bisa Sanya Hoton Matarsa ta na Sunbatar sa a Facebook

0
93

Muslmai magoya bayan dan wasan kwallon kafar Super Eagle, Ahmed Musa sun bayyana rashin jin dadinsu bayan hoton da dan wasan ya wallafa yana sumbatar matarsa a shafinsa na Facebook.

Hoton dai ya nuna matar dan wasan na sumbatar kumatunsa.

Musulmai magoya bayan dan wasan sun zarge shi da yin abunda ya sabawa koyarwar addininsa.

Sun bukace shi da ya tuba kuma ya cire hoton.

Kaptin na Super Eagles ya dora hoton ne a Facebook don taya murna ga matarsa da dansa kafin mutane su fara bayyana ra’ayinsu cikin bacin rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here