An Sanya Dokar Kayyade Kayan Lefe Da Gara a Garin Kanya Babba, Jihar Jigawa

0
354

Sashin Hausa na muryar Amurka(VOA Hausa) ya wallafa labarin cewa,hukumomin wani gari a jihar Jigawa a arewacin Najeria na kokarin saukaka aure tsakanin ‘yan mata da samari ta hanyar kayyade wasu abubuwan al’ada da ake yi.

Mahukunta a wani gari da ake kira Kanya Babba ko Talatar Kanya a karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa sun sanya wata sabuwar doka dangane da tsare-tsaren aure, musamman na ‘yan mata da samari.

Ita dai wannan doka ta ta’allaka ne akan kayyade kayan lefe da saurayi kan kai wa budurwa da kuma gara da iyayen amarya kan kai wa gidan ango.

Dokar ta tanadi a yi matsakaicin akwati guda daya mai dauke da atamfofi hudu, leshi daya, shadda daya, gyale daya, hijabi biyu, takalmi da jakar hannu guda daya, kayan kwalliya da sauran ‘yan tarkacen da za a hada cikin wannan akwati.

Dokar ta kuma bukaci a kai kayan lefen wurin daurin aure a gaban waliyyan amarya da ango, da mahukunta da sauran jama’a domin tabbatar da an kiyaye dokar.

Bashari Makama, shi ne mataimakin sakataren kwamitin dokar, ya ce sun kafa dokar ne duba da yadda rayuwa ta yi tsada da kuma yawan ‘yan mata da samari da ke garin domin kawo saukin aure ga dukkan bangarorin.

Sai dai wasu iyaye mata sun ce dokar ka iya kawo rashin darajanta mace a gidan aure, ganin cewa an sauwaka lefe.

Wannan tsarin ya sha bamban da yadda ake yi a wasu yankunan arewacin Najeriya inda wasu ke kai akwati uku ko shida, har zuwa sha biyu 12 makare da kaya bisa nauyin aljihun masu auren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here