An Kara Sace Yaro Dan Shekara 9 a Kano yayin da aka Ceto yara 7 da aka Siyar da su a Anambra da Enugu

0
163

Wani yaro Dan shekara 9, mai suna Yusuf Nasiru dan unguwar Kawaji ya bata a yayin da aka ceto yara 7 da aka sace daga Kano a ka siyar da su a Jihohin Enugu da Anambra.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, an sace yara da dama a yankin, wanda hakan ya zama babbar matsala a Kano.

An sace yaron mai suna Yusuf a ranar 28 ga watan Disamba bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da misalin karfe 6:25.

Idan za’a iya tunawa dai a watan Oktoba na shekarar 2019 ne rundunar yan sanda reshen jihar Kano tayi holen wasu mutane su 6 da ake zarginsu da sacewa, siyarwa tare da sauyawa yara 9 addini.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin bincike kan batun satar yara a jihar.

Yayin da yake sanar da ceto yara 7 a yau Litinin, kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya shaidawa BBC Hausa cewa kwamitin ne ya yi akin ceto yaron bayan ya ziyarci gidajensu a jihohin Anambra da Enugu.

Ya ce, iyayen yaran sun gane ‘ya’yansu sannan za’a mika su gare su nan bada jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here