Akwai Yiwuwar Ba za a Koma Makarantu ranar 18 ga Watan Janairu ba – Gwamnatin Tarayya

0
1087

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sauya ranar komawa makarantu ta 18 ga watan Janairu, biyo bayan samun yawaitar masu kamuwa da cutar Korona.

Kwamitin yaki da cutar Korona ne dai ya bada umarnin rufe makarantu har zuwa 18 ga watan Janairu na 2021.

Sai dai yayin taron jawabi da kwamitin ke yi yau a Abuja, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana damuwa kan ranar da aka tsara komawa makarantun.

“Ranar 18 ga watan Janairu da aka sa na sake bude makarantu ba wai hakan ya zama yayi kyau bane. Yayin da muka yanke shawarar wannan ranar mun yi ne don cimma burin abinda muke aiki akan sa”, inji shi.

Adamu Adamu ya kara da cewa, “Kwarai, muna duba kan ranar kuma muna duba kan abubuwan dake faruwa cikin al’umma. Ko a yau a taron kwamitin yaki da Korona mun lura da yadda ake samun yawaitar masu kamuwa da cutar tare da yin tunani idan zamu sake yin wani duba kan sake bude makarantu”.

“Kan batun komawa makarantu ranar 18 ga wata, muna duba a kai, zamu sake duba……gobe ma’aikatar ilimi za ta dau matsaya akai”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here