Ƴan Bindiga Sun Kashe wani Mutum a Unguwar Zoo road Dake Kano

0
579

Wasu yan bindinga da ba’a san ko suwaye ba sun dira a wani kamfanin shinkafa a Kano tare da harbe wani mutum a daren jiya Asabar.

Mutumin mai suna Alhaji Isa Abubakar, ya rasu ne sa’o’i kadan bayan an harbe shi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana.

Wata majiya ta shaidawa jaridae Sahelian Times cewa, yan bindigar sun dira kamfanin shinkafar ne dake titin Zoo road kusa da Ado Bayero Mall a dare.

“Sun yi yunkurin fitar da mutumin daga motarsa, sai dai yaki fita. Sai kawai suka jefo shi daga motar suka harbe shi a kirji”, inji wani mutum da abin ya faru akan idonsa.

Majiyar ta kara da cewa, maharan sun gudu da motar mutumin tare da barinsa kwance cikin jini a kan titi.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ya ce an yi gaggawar kai mutumin asibiti don kula da lafiyarsa.

Kodayke, mutumin ya rasu a asibiti, sa’o’i kadan, sakamakon jinin da ya fita daga jikinsa na harbin bindiga da aka yi masa.

Wata majiya daga iyalan mamacin sun tabbatar da cewa, za’ayi jana’izar sa da safiyar yau Lahadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here