Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Mun Shirya Gudanar da Zaɓe a Kano – KANSIEC

0
181

Jam’iyyun siyasa 12 ne suka gabatar da yan takarkarunsu a yayin da ake shirin gudanar da zaben kananan hukumomi ranar 16 ga watan Janairu a Kano.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN), yau Asabar a Kano.

Garba Sheka ya ce hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye don tabbatar da an gudanar da zaben kamar yadda dokar zabe ta tanada.

Ya ce za’a gudanar da zaben a kananan hukumomi 44 da kujerar Kansiloli 484 dake jihar.

Ya ce, hukumar ta tattauna da shugabannin jam’iyyu da masu ruwa da tsaki kan zaben don bayyana irin shirye-shiryenta.

“Mun fara raba kayan aiki zuwa ga ofisoshinmu na kananan hukumomi, sannan muna kai kayan aiki masu muhimmanci a sannu a hankali.

“Hukumar ta kuma bada horo ga jam’an zabe da sauaran ma’aikata don basu dama wajen yin aikinsu yadda yakamata.

” Nasarar zaben nan nauyi ne akan duk masu ruwa da tsaki. Haka kuma muna neman hadin kan kowa don gudanar da zaben”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here