Safara’u: Dalilin Da Yasa Aka Sauya ni a Shirin ‘Kwana Casa’in’ – Safiyya Yusuf

0
636

Safiya Yusuf jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood wacce ta fito a shirin Kwana Casa’in da ake haskawa a tashar Arewa 24 duk sati a tattaunawa da Jaridar Weekend Magazine ta yi bayanin dalilan da yasa aka cireta a shirin.

A labarin da jaridar ta wallafa ta ambato Safiyya Yusuf wacce ta fito a shirin Kwana Casa’in a sunan Safara’u ta na bayyana irin rawar da ta taka a shirin.

“A shirin Kwana Casa’in na fito a matsayin budurwa yarinya wacce ke karatu don zama likita.”

A cikin shirin, Mahaifiyarta ta na fama da ciwon kafa don haka take son zama likita don kula da lafiyarta da taimakon mutane.

A gefe guda kuma mahaifinta baya son tayi karatu yafi so tayi Aure saboda zai samu kudi daga wanda ta Aura.

Safiyya wace ta bayyana burinta na zama mai bada umarni ta ce, “Ina so na zama mai shirya fim ko mai bada umarni”.

Da aka tambayeta shin za ta iya taka rawa a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood?
Sai ta ce” Eh, zan so hakan sai dai akwai wuraren da bazan iya ba. A matsayina na Muslma dole na girmama wasu dokoki. Amma zan iya taka rawa a Nollywood idan aka bani dama. Ina son fina-finansu.

Dangane da yadda aka sauya ta a shirin ‘Kwana Casa’in’ kuwa, Safiyya ta bayyana cewa taji rashin dadi a lokacin.

“Naji dadi da rashin dadi a lokaci guda. Dalilin da yasa naji dadi shi ne yadda mutane suka dinga bayyana ra’ayinsu suna cewa baso son sabuwar Safara’u, amma naji dadi yadda mutane suka dinga magana akaina da yadda suke kewata. A dai-dai lokacin kuma naji ba dadi saboda bani da damar taka rawa a shirin. Abubuwa da dama sun faru, akwai rashin fahimta.amma abinda ya faru ya riga ya faru.

Safiyya Yusuf ta kuma yi karin bayani kan dalilin da yasa aka sauyata a shirin.

“An sauya ni ne saboda bani da lafiya sosai a lokacin da ake daukar shirin. Sun fara daukar shirin amma bana wajen saboda bani da lafiya kuma basu da wani zabi face su sauyani a lokacin. Wannan shi ne dalilin.

An tambaye kan wani faifan bidiyo na tsiraici dake yawo a kafafen sadarwa na zamani kan mene ne ra’ayinta akai.

“Na mayar da martani ta hanyar yin shiru. Ban ce komai ba a shafukan sadarwa na zamani. Abin da yazo raina shi ne hakan alama ce ta cewa zan samu nasara a rayuwata ta gaba. Allah yasan abin da yake mai kyau ko mara kyau gare ni kuma yasan kaddarata. An ta matsamin akan sa amma ban sanar da kowa irin halin da nake ciki ba. Kawai na mika lamarin ne ga Allah”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here