Ganduje Ya Ziyarci Gidan su Kwankwaso Don yin Ta’aziyyar Mahaifinsa

0
551

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Makaman Karaye, Mahaifin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a gidansa dake garin Kwankwaso karamar hukumar Madobi.

A yayin ziyarar, Ganduje ya bayyana cewa, “Mun rasa Uba mai kulawa. Wanda ya samu shekaru masu albarka kafin rasuwarsa. Allah ya jikansa Allah ya yi masa Rahma”.

Ganduje ya kara da cewa, ” Babanmu mutum ne na kwarai, mai hakuri, shugaba mai saukin kai, wanda kuma yake hidimtawa al’umma. Allah ya yafe masa laifukansa yasa Aljanna makomarsa”.

Yayin da gwamnan ke mayar da martani kan bukatar da kanin Sanata Kwankwaso ya yi na barin matsayin makaman karaye ga ahalin mamacin, Ganduje ya ce “Babu bukatar yin wannan rokon, saboda wannan gida ya chan-chanci samun komai daga gare mu. Koyaushe muna girmama wannan gida”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here