Za’a yiwa Buhari da Osinbajo Allurar Rigakafin Korona

0
104

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, shugaban hukumar ci gaban lafiya a matakin farko na Najeriya, Faisal Shuaib, ya bayyana cewa Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa, Yemi Osinbajo za su kasance cikin rukunin farko da za a yi wa riga-kafin korona na kamfanin Pfizer/BioNTech da ƙasar ta amince a yi amfani da shi.

Mista Shuaib ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin jawabin da kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa kan yaƙi da cutar korona.

Ana sa ran cewa zuwa ƙarshen watan Janairu wannan riga-kafin zai isa ƙasar kuma kusan guda 100,000 za su fara isa a karon farko.

Tuni dama kwamitin ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya da ke kan gaba wurin yaƙi da cutar da tsofaffi masu shekaru ne za su fara amfana da wannan riga-kafin.

Baya ga Shugaba Buhari da mataimakinsa, akwai manya da ke cikin gwamnati irin su sakataren gwamnatin tarayya wato Boss Mustapha wanda yana cikin waɗanda za a yi wa riga-kafin domin mutane su gani kuma su yarda a yi musu.

Ya kuma yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa shugabanni za su zama na farko wurin karɓar wannan riga-kafin, inda ya ce ba ƙasar da ke so ta ga jogororinta korona ta kashe su.

Ya kuma bayyana cewa ko a wurin yaƙi, idan mutum yana so ya ga bayan maƙiyansa, abu na farko da yake yi shi ne kai hari ga shugabanni, da janarori, da an yi hakan, duka sauran sojojin jikin su zai mutu, in ji shi.

A cewarsa, domin gudun haka, ƙasar za ta bai wa shugabanninta a faɗin ƙasar wannan riga-kafin a karon farko domin kada a bar shugabannin ƙasar cikin hatsari.

Ya kuma bayyana cewa hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna wato NAFDAC, sai ta tantance riga-kafin tukuna a fara amfani da shi a ƙasar.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da annobar korona, Boss Mustapha, ya ce ganin yadda ake yawan samun ƙaruwar wannan cuta, ya zama dole mutane su ƙara taka tsan-tsan.

Shi ma ɗaya daga cikin masu jagorar wannan kwamiti, Sani Aliyu, ya bayyana cewa idan aka ci gaba da samun ƙaruwar masu kamauwa da wannan cuta ya zama tilas ga ƙasar ta sake saka dokar kulle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here