Korona: Gwamnatin Tarayya Za ta Kara Sanya Dokar Kulle

0
155

Gwamnatin tarayya a jiya Alhamis ta ce bata da wani zabi face ta kara sanya dokar kulle a kasar matukar aka ci gaba da samun yawaitar masu kamuwa da cutar Korona.

Babban jami’in tsare-tsare na kwamitin yaki da Korona, Dr.Sani Aliyu ne ya yi bayanin haka yayin jawabin da kwamitin keyi a Abuja.

Sai dai a ranar Litinin din da ta gabata ne aka jiyo ministan yada labarai, Lai Mohammed na cewa, gwamnatin tarayya ba ta da shirin sanya dokar kulle a yayin da kasarnan ke fama annobar Korona zagaye na biyu.

Sai dai yayin da yake jawabi a jiya Alhamis, Babban jami’in tsare-tsaren kwamitin, ya ce yawaitar samun masu kamuwa da cutar a yan kwanakin nan abin damuwa ne kuma akwai bukatar a sanya dokar kulle.

Dr. Sani Aliyu ya ce “Idan aka ci gaba da samun masu kamuwa da cutar kuma aka samu mace-mace, bamu da wani zabi. Idan bama bukatar kulle, yanzu lokaci ne da zamu tabbata mun bi ka’idojin da aka shimfida”.

Shima anasa jawabin shugaban kwamitin na yaki da Korona, Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce ” Kwamitin ya damu matuka kan yadda ake samun yawaitar masu kamuwa da cutar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here