Kotu ta dakatar da Ganduje daga Zaftare Albashin Ma’aikatan Shari’a

0
79

Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga zaftare albashin  ma’aikatan shari’a har zuwa kammala sauraron karar da aka gabatar gabanta.

Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda suka shigar da karar sun hada da: Mukhtar Rabiu Lawan, Sule Aliyu, Sani Yau, Zahran A Fagge, Yahaya Muhammad Sani, Hussaini Imam Galadanchi, Bashir Lawan Abdullahi, Haruna Ahamed, Kabiru Usman Danbatga, Fatihu Wada Khalil, Auwal Nidi Sitti, Auwalu Mohammed, Abubakar El-Yakub da Sani Lamido da suka shigar da kara a madadin kansu da kuma wakilan kungiyar ma’aikan shari’a na kasa reshen jihar Kano.

Inda suke karar, gwamnan jihar Kano, kwamishinan shari’a kuma antoni janar, kwamishinan kudi, shugaban ma’aikata na Kano da Akanta Janar na Kano.

Masu karar sun kai karar ne bisa zafare musu albashinsu na watannin Nuwamba da Disamba.

Ma’aikatan sun kuma nemi a dawo musu da kudin da aka zaftare na watanni biyun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here