Hukumar Zaɓe ta KANSIEC Ta Gaza Cire Sunayen Ƴan Takarar da Aka Samu da Ta’ammali da Muggan Kwayoyi

0
261

Har yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano(KANSIEC) ta gaza cika alkawarin da ta dauka na soke chan-chantar duk wani dan takara da aka samu yana mu’ammala da muggan kwayoyi, yayin da saura kwanaki 10 a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Idan za’a iya tunawa dai, kwamandan hukumar dake yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Kano, Dr. Ibrahim Abdul ya sanar da cewa ofishinsa bayan tantance yan takarkarun shugabancin kananan hukumomi, an samu mutane 6 dake ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Dr. Ibrahim Abdul, ya ce “Mun mika sunayen wadanda aka samu suna shan miyagun kwayoyi ga gwamnatin jiha kuma muna jiran karbar sabbin sunaye don kara tantancewa”.

Duk da saura kwanaki kadan a gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano, hukumar zabe ta KANSIEC da gwamnatin jihar har yanzu basu fitar da wani bayani kan binciken na hukumar NDLEA din ba.

Tunda farko shugaban hukumar zaben, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, ya yi alkawarin cewa duk dan takarar da aka samu yana ta’ammali da miyagun kwayoyi za’a soke chan-chantarsa.

Kari kan hakan, duk yunkurin da muka yi na jin ta bakin shugaban hukumar zaben yaci tura, yayin da wadanda aka samu da shan miyagun kwayoyin ke ci gaba da yakin neman zabe.

A wani bangaren kuma, jam’iyyar PDP dake biyayya ga tsohon gwamna, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso sun yi barazanar daukar matakin shari’a kan hukumar zaben matukar aka yi amfani da tambarin jam’iyyar takardar zabe a zaben dake tafe.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da tsagin Aminu Wali ke jadaddda cewa za su shiga zaben, bayan tsagin Kwankwasiyya sun kauracewa zaben.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Sanusi Sirajo Kwankwaso ya ce “Duk wanda muka samu ya yi amfani da tambarin jam’iyyarmu zai amsa gayyatar kotu saboda mun shirya tafiya kotu don kare jam’iyyarmu, dalili shi ne a matsayinmu na halatttun shugabannin jam’iyya mun yanke shawarar baza mu shiga zaben ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here