
Wata Amarya mai suna, Fatima Hassan Fari ta rasu a ranar daurin Aurenta a karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa, Fatima ta rasu da misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Janairu sa’o’i uku kafin a daura aurenta kamar yadda Jaridar The Nation ta rawaito.
An binne ta da karfe 2 na rana a ranaf ta Asabar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Yayin da kawaye da yan’uwa su ka dinga bayyana alhinin rasuwarta a shafukan sadarwa. Wani abokin karatunta, Mallam Muhammad Sani Isah, ya bayyana Fatima a matsayin budurwa mai jin kai da tausayin al’umma.