2023: Ba wa Osinbajo Da Zulum Takarar Shugabancin Ƙasa ne Kaɗai Zai sa APC ta yi Nasara – Jigo a Jam’iyyar

0
110

A yayin da zaben shekarar 2023 ke karatowa, wani jigo a jam’iyyar APC, Sanata Abubakar Gerei, ya ce ba wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Babagana Zulum gwamnan jihar Barno takara ne kadai zai tabbatar da nasarar jam’iyyar APC.

Sanata Girei, ya ce idan APC za ta mika takarar shugaban kasa ga yankin kudancin kasarnan, zai fi dacewa ta ba wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo takara don ci gaba da aiwatar da manufofin shugaba Buhari da kuma bawa Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum takarar mataimakin shugaban kasa.

Jigon jam’iyyar ta APC wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna kan batutuwan da su ka shafi kasa, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su kaucewa yin kuskure a zaben dan takara a jam’iyyar.

“Idan mutum kamar Osinbajo zai hadu da Farfesa Zulum, ba makawa zamu samu nasarar lashe zaben”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here