Yanzu-Yanzu: Jami’ar Bayero ta Sanar da Ranar Komawa Makaranta

0
340

Jami’ar Bayero ta amince da soke zangon karatu na shekarar 2019-2020.

Hakan na dauke ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Fatima Binta Mohammed.

Takardar ta ce, sabon zangon karatu zai fara daga ranar 18 ga watan Janairu a zango na farko, yayin da zango na biyu zai fara 3 ga watan Mayu na 2021.

Daliban dake karatu mai zurfi kuwa, za su fara karatun zango na farko ne daga ranar 18 ga watan Janairu yayin da zango na biyu zai fara daga daya ga watan Yuni.

 

Akwai Karin bayani nan gaba…….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here