Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Ya Rasu

0
246

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdullahi Karaye ya rasu.

Ya rasu a yau Litinin ya na da shekaru 96.

Mai magana da yawun masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa, a wata sanarwa da ya fitar ya ce tshohon kakakin majalisar ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa dake Karaye.

Mamacin ya kasance shugaban majalisar dokokin jihar Kano daga 1979 zuwa 1983.

Ya rasu ya bar mata biyu da ya’ya shida da jikoki da dama.

Haka kuma, Sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar ne ya jagoranci jana’izarsa.

Daruruwan Muslmai ne suka halarci jana’izar a fadar Sarkin Karaye.

Sanarwar ta ce an binne shi a makabartar Limanci dake garin Karaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here