Jami’ar Benin dake Jihar Edo Ta Sanar da Ranar Komawa Makarantar

0
109

Hukumomin jami’ar Benin(UNIBEN) dake jihar Edo sun umarci dukkan sabbi da tsofaffin daliban makarantar da su dawo karatun zangon karatu na shekarar 2019/2020 da Zangon karatu na shekarar 2020/2021 a ranar 30 ga watan Janairu.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar, Benedicta Ehanire ya fitar bayan kammala taron majalisar zartarwar jami’ar a yau Litinin.

Jami’ar ta ce zangon karatu na farko na kakar karatu ta 2019/2020 zai kai har 1 ga watan Afrilu, yayin da zango na biyu zai fara daga 5 ga watan Aprilu.

Jami’ar ta kuma gargadi dukkan daliban da za su dawo karatu da su bi dukkan matakan kariya daga cutar Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here