Gidan Badamasi: Rumbun Nishaɗi, Rumfar Faɗakarwa

0
327

Daga Musa Sani Aliyu

Gidan Badamasi fim ɗin da akewa laƙabi da  ‘Maganin hawan jini kyauta’ fim ne mai nisan zangon dake zama ɗaya tilon dake ci gaba da haskaka hasken ruhin nishadin dubban masu kallo.

Yau 04/01/2021 yayi dai-dai da ranar da ake ci gaba da daukar zango na uku. Kamar yadda aka sani zango na farko da zango na biyun fim din Gidan Badamasi yazama kyakkyawar nasara, a inda ya nishantar ya kuma fadakar da masu kallo cikin wani salo mai ban sha’awa da sanya shashshauqan shauqi.

Fim din barkwancin wanda Falalu A. Dorayi ya bada umarni, Nazir Adam Salihi ya dauki nauyi tare da tallafin Dorayi Film And Distribution Limited, fim ne daya hadar da manyan jarumai irinsu: Jaruma Hadiza Gabon, Magaji Mijinyawa, Mustapha Nabaruska, Nura Dandolo, Ado Isah Gwanja, Tijjani Asase, Hauwa Ayawa da dai sauransu.

Kamar yadda shafin Labaran Kannywood suka wallafa a shafin su,sun rawaito cewar Jarumi kuma mai bada umarni Falalu A.Dorayi ya bayyana cewa wannan karon,shakka babu a shirya yin dariya cikin rumbun kyakyatawa fiye da zango na daya dana biyu dasu gabata ninkin ba ninki.

Fim din Gidan Badamasi fim ne da aka ginashi bisa tubalin nishadin dake nuna yadda wani uba ya hana ahalin sa rawar gabar hantsi da dumbin dukiyar daya tara, a yayin da a gefe guda ‘ya yan sa ke da buri tare da tsantsar, tsabar tsagwaron fatan ganin ya kwanta dama.

Karku sake a baku labarin GIDAN BADAMASI ZANGO NA UKU.

Ku shirya ganin zallan nishadi, nagartattun maganganu, da zasu saku zaman dirin dirshan din kyakyata DARIYA daku da iyalan ku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here