A Gobe Talata Za’a Fara Shirin Ɗaukar Ma’aikata 774, 000 – Keyamo

0
228

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago ya ce tsarin aiki na musamman wanda za’a dauki yan Najeriya 774, 000 aiki zai fara ne a gobe Talata.

Keyamo, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter ya ce shugaba Buhari ne ya amince da ranar.

“Shugaban Kasa Buhari ya amince da fara shirin daukar ma’aikata na musamman 774, 000, tsarin da za’a dauki yan Najeriya marasa aikin yi zai fara ne gobe Talata 5 ga watan Janairu, na shekarar 2021″, inji shi.

” Dukkan ofisoshin hukumar NDE a jihohi sun shirya fara aikin”.

Tsarin na daukar ma’aikata ya haifar da rashin jituwa tsakanin ministan da yan majalisar wakilai.

Shirin dai an tsara shi ne don daukar ma’aikata 1,000 daga kowacce karamar hukumar a kasarnan.

Wadanda za su amfana da shirin za su dinga karbar dubu 20 duk wata.

An ware Naira Biliyan 52 don aiwatar da shirin a kasafin kudi na shekarar 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here