Yanzu-Yanzu: An Dakatar da Kwamishinan Muhalli Bisa Zargin yin Lalata da Budurwarsa

0
504

Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da kwamishinan muhalli, Abiodu Abudu-Balogun.

An dakatar da Mista Abudu-Balogun daga aiki ne bisa zargin  cin zarafin budurwarsa mai shekaru 16 ta hanyar lalata mai suna Barakat Mayowa Melojuekun.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Mista Tokunbo Talabi ya fitar, ya sanar da cewa an dakatar da kwamishinan ne don sauraron kwamitin bincike da aka kafa kan zargin.

Ya yi bayanin cewa, gwamnatin jihar ta dakatar da Abudu-Balogun ne don bashi dama wajen bayar da cikakken hadin kai ga kwamitin bincike da yan sanda ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here