Yanayin Sanyi: An Bukaci Al’umma da Su dinga Tallafawa Marayu da Kayan Sanyi

0
225

An buƙaci al’umma dasu ke tallafawa marayu da mabuƙata da kayan sanyi a wannan lokaci Dan su samu suturta kansu da kare lafiyarsu -Danlarabawa

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe ( Grassroot Care & Aid Foundation GCAF ) Ambassador Auwal Muhd Ɗanlarabawa ne yayi wannan Kira a lokacin da suke raba kayan sanyi ga yara marayu guda 3000 a kananan hukumo shida dake jihar Kano.

Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa ya ce shekaru goma kenan suna gudanar da wannan aiki a kowanne lokaci na sanyi kuma har yanzu Cikin ikon Allah Ana Cigaba da wannan aiki na tallafawa marayu bayan ɗaukar nauyin karatun su da akeyi tsawon lokaci Mai yawa.

Ɗanlarabawa ya ce akwai bukatar al’umma suyi koyi da wannan aiki a unguwanni ta hanyar zakulo yara marayu a Tallafawa rayuwarsu a kowanne mataki na rayuwa musanman wajen tarbiyya da ilmi hakan zai taimaka a samu yara masu tasowa na gari kuma abin alfahari.

A ƙarshe Ɗanlarabawa yayi godiya ga daukacin al’ummar dake Aiko musu da tallafi da ɗaukar nauyin marayu dama bawa Gidauniyar gudunmawa a Koda yaushe Dan Cigaba da gudanar da ayyukan Jin ƙai da ceton Mabuƙata.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here