Korona: Gwamnatin Tarayya ta Sanya Takunkumin Hana Tafiye-Tafiye Ga Yan Najeriya 100

0
111

Gwamnatin tarayya ta wallafa bayanan fasfodin matafiya 100 da suka gaza bin ka’idojin hana yaduwar cutar Korona, inda ta sanya mu su takunkumin hana tafiye-tafiye na watanni 6.

Rahotanni sun bayyana cewa Matafiyan da abun ya shafa, sun ki yarda ayi musu gwajin cutar Korona yayin da suka dawo Najeriya.

Tun da farko dai, gwamnatin tarayayya ta yi ikirarin tsaurarawa ga mafatafiyan da suka kaucewa bin ka’idojib hana yaduwar cutar Korona.

Don tabbatar da ikirarin nata, gwamnatin tarayya ta sanya takunkumin hana tafiye-tafiye ga yan Najeriya 100.

Kwamitin yaki da korona na fadar shugaban kasa, ne ya wallafa bayanan mutanen a ranar Asabar

Sanarwar da kwamitin ya fitar ta ce takunkumin ya fara ne daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2021 zuwa 30 ga watan Yuni.

Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa, wadanda abun ya shafa an sanar da su kuma za’a hana su fita kasarnan a dai-dai lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here