An Kwantar da Bola Tinubu a Asibitin Birnin Paris, Sai dai Baya Dauke da Cutar Korona

0
142

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, an kwantar da Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas a Asibitin birnin Paris na kasar Faransa bayan ya kamu da rashin lafiya.

Kodayake rahotanni sun bayyana cewa, baya dauke da cutar Korona.

Gwajin da aka yiwa Tinubu kafin ya tafi kasar Burtaniya ya nuna baya dauke da cutar.

Jaridar ta TheCable ta ce an fada mata cewa Tinubu yana kokawa kan gajiya dake samunsa don haka ya yi tafiya don ya huta.

Ya tafi birnin Paris a karshen mako don duba lafiyarsa.

Tunde Rahman, mai magana da yawunsa ya karyata cewa, Jagoran APCn cutar Korona ta kama shi.

“Wannan labarin ba gaskiya bane. Asiwaju yana koshin lafiya kuma baya dauke da cutar Korona”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here