Akwai Alaƙa Mai Kyau Tsakanina Da Kwankwaso – Shekarau

0
100

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce yana da kyakkywar alaka tsakaninsa da gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sanata Shekarau na fadin hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai yau Lahadi a Kano.

Ya ce babu wani rashin jituwa tsakaninsa da Ganduje ko Kwankwaso.

“Ni da Ganduje mun kasance tare tsawon shekaru. Yayin da nake a matsayin Sakataren din-din-din, lokacin yana kwamishina, kuma mun yi aiki tare.

“Ina son tabbatar muku cewa alakarmu tana nan daram har zuwa yanzu. Don haka babu wata matsala tsakaninmu.

” Haka abin yake da Kwankwaso; muna da kyakkywar alaka. Banbancin siyasa bai zai shafi alakarmu ba. Ban taba barin wata jam’iyya saboda shi ba.

“Lokacin da ina APC, Kwankwaso ya shiga jam’iyyad, na bar ta ba saboda shi ba, sai don shugabannin jam’iyyar. Irin haka ne ya faru a PDP, na bar ta ba don ya shiga jam’iyyar ba”, ini shi.

Shekarau ya kuma kara yin kira ga masu zabe da su dinga duba kan nagartar shugabanni yayin zabe, mai makon duba yankin da suka fito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here