Mai Palace Ya Kai Ziyarar Duba Ayyukan da yake yiwa Al’ummar Mazabarsa

0
52

 

Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, Dan majalisar tarayya Mai Wakiltar Kananan hukumomin Gusau da tsafe,  ya kai ziyarar gani da ido ta aiki a garin Kwarin gwanuwa dake karamar hukumar mulki ta tsafe.

Mai Palace yakai ziyarar ne a makarantar firamare dake garin domin duba irin aikin da ya samo na gyara Makarantar karkashin wakilcin sa.

A cikin jawabinsa ga al’ummar garin Mai Palace ya ce, ” wannan aiki aikine Wanda zai amfani dukkanin al’ummar wannan gari yana da kyau ku hada kan ku batare da bambanci siyasa ba domin ganin kun kula da duk wani cigaba da za’a kawomaku a gwamnatacce”.

Daga karshe Mai Palace yayi godiya akan al’ummar Kwarin Ganuwa da irin fatan alheri da kuma goyon bayan da suke bashi.

 

Daga garin Danjigba dake Karamar Hukumar Mulki ta tsafe, kuwa, Hon. kabiru amadu Mai Palace Dan majalisar tarayya Mai Wakiltar Kananan hukumomin Gusau da tsafe, ya kai ziyara wannan gari kai tsaye inda ya isa fadar uban kasar garin domin tattaunawa dashi akan abubuwan da suka shafi al’ummar garinsa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here