Jami’in Ɗan Sandan da Yaƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 864 ya Ajiye Aiki

0
122

Wani jami’in dan sanda wanda ya ce yaki karbar toshiyar baki ta Naira Miliyan 864 ya ajiye aikinsa inda yayi ikirarin cewa anki yi masa karin girma.

Jami’in mai suna, Francis Erhabor, dake shugabantar ofishin yan sanda a jihar Akwa Ibom kafin ya ajiye aikin nasa.

Shafin, Igbere TV ne ya wallafa labarin ajiye aikin ma’akacin a yau Asabar.

Shafin na Igbere TV a watan Disamba ya karrama Mista Erhabor a matsayin ‘Gwarzon Dan sanda na shekara’ inda ta ce dan sandan ya lashe zaben zama gwarzo.

“Ina ganin wadanda ke kasana suna samun karin girma sama dani sosai da sosai, kuma abin yana bani takaici. Na mika sakon korafi kuma an bincika an tabbatar da hakan, amma har yanzu ba abinda aka yi” inji mista Erhabor.

“Na bata shekaru 30 ina bautawa kasata”, inji shi.

Mista Erhabor ya ce ya zama dan sanda tun shekaru 30 da suka gabata a shekarar 1990 yayin da yake karami dan shekara 17.

Ya ce an fada masa a lokacin cewa, ” Rundunar yan sanda na bukatar saurayi irinsa wanda ke da kishin kasa da son yin aiki”.

Wani jami’i a ofishin yan sandan a garin Oyu ya tabbartwar da jaridar PREMIUM TIMES cewa Erhabor ya ajiye aiki.

Sai dai rundunar yan sanda a jihar ta karyata labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here