Gwamnatin Jihar Ebonyi ta Bada Umarnin Komawa Manyan Makarantu a Jihar

0
93

Gwamnatin Jihar Ebonyi ta umarci dukkan makarantu a jihar da su dawo karatu a ranar 18 ga watan Janairu don ci gaba da zangon karatu na shekarar 2020/2021.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Dr. Onyebuchi China ya fitar a yau Asabar a birnin Abakaliki.

Kamfanin dallancin labarai na kasa(NAN) ya rawaito cewa jihar ta Ebonyi ta umarci makarantu da su tafi hutun bikin Kirisimeti a ranar 18 ga watan Disamba, bayan ta sake bude makarantun a watan Oktoba tare da janye dokar kulle da cutar Korona ta haifar.

“Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi ya umarce ni da na sanar da al’umma cewa an daga ranar komawa makaranta daga 4 ga wata zuwa 18 ga watan Janairu.

“Dagawar ta faru ne sakamakon bukatar daukar matakan kariya daga cutar Korona kamar yadda kwamitin yaki da Korona na fadar shugaban kasa ya bada umarni”, inji Chima.

Sanarwar ta kara da cewa, manyan makarantu a jihar za su koma harkokin karatu a ranar Litinin 4 ga watan Janairu bisa tsarin bin matakan kariya daga cutar Korona.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, an yanke shawarar bude manyan makarantun ne bayan kungiyar ASUU ta janye yajin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here