Na Koyi Darusa A Soyayya da Dangote -Tsohuwar Budurwarsa

0
771

Wata budurwa yar Atlanta ta kasar Amurka mai suna Bea Lewis ta bayyana yadda soyayyar shahararen attajirin Afrika, Aliko Dangote ta mamaye zuciyarta, inda ta ce ta dauki darasi da dama cikin alakarsu ta soyayya.

Ta kuma ce soyayyar ta su ta haifar mata da abu mai kyau duk da rabuwar da suka yi.

Ms Lewis ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram inda ta shawarci mutane da su dinga nuna soyayya ba tare da tsammanin burin wani abu ba.

“Na yi soyayya da wanda yafi kowanne bakar fata kudi a Duniya. Ya karya zuciyata zuwa gida 1000.

“Na koyi darasi daga gareshi fiye da yadda na koya daga mutanen da na hadu da sh.

“Tattaunawa da Attajirin mai kudi a kullum yana sa kaga duniyar da ban-banci fiye da yadda ka fara rayuwa a birnin Liberty.” Inji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here