Jam’iyyar PRP Ta Taya Ƴan Najeriya Murnar Bikin Sabuwar shekara Tare Da Bayyana gazawar Gwamnatin Buhari

0
196

Jam’iyyar PRP ta taya yan Najeriya murnar Bikin Sabuwar Shekara ta 2021.

A wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Falalu Bello, OFR wacce aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS a yammacin jiya Laraba daga jami’in yada labarai na jam’iyyar na kasa, Alhaji Abdul-Kadie Abubakae Kurawa.

Jam’iyyar ta PRP ta bayyana shekarar 2020 a matsayin wacce tafi kalubale a tarihin duniya saboda yadda ta ke tattare da batutuwan da suka shafi harkar lafiya da karyewar tattalin arziki.

“Shekarar 2020 na daya daga cikin shekaru mafiya wuya, ba iya Najeriya kadai ba har duniya gabadaya. Annobar Korona da alakarta da tattalin arziki da kalubalen fannin lafiya ta zama abin damuwa ga kowa”, inji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma jajanta yadda yan Najeriya ke shan wuya tsawon shekaru na mulkin shugaban kasa Buhari, “baza mu mantawa da da irin wahalhalu da matsi da gwamnatin Buhari da APC su ka samu a ciki ba tun daga shekarar 2015″, inji ta.

Malam Falalu ya bukaci shugaba Buhari da APC su mayar da hankali wajen warware matsalolin da al’umma ke ciki.

Jam’iyyar PRP ta ce, Yan Najeriya za su dora alhakin abinda ke damun yan kasa kan gwamnatin ” Mista Integrity”.

Sannan ta yi kira ga yan Najeriya da su hada kai da goyan bayan manufofinta don ganin an samar da ci gaban Najeriya anan Gaba.

Jam’iyyar ta kuma taya yan Najeriya Murnar bikin Sabuwar Shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here