2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Kasa na Yahaya Bello Sun Mamaye Birnin Kano

0
151

A yayin da zaben shugaban kasa na shekarar 2023 ke karatowa, fastocin neman takarar shugaban kasa na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello sun bayyana kan tituna a jihar Kano a safiyar yau Alhamis.

A wani abu da yazo a mamaki ga mutanen Kano, fastocin gwamnan jihar Kogi an lika su a wasu sasssa na birnin Kano inda yake neman takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

Hotunan takarar sun bazu zuwa wasu sassan kwaryar cikin birnin Kano.

Fastocin dai babu tambarin jam’iyya sai dai hoton Yahaya Bello na Neman takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Fastocin dake dauke da Rubutun “Yahaya Bello Don Kawo Sauyi bai daya” an sanya su a guraren da al’umma suka fi hada-hada.

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar Nigerian Youth Awareness ne su ka dauki nauyin buga Fastocin.

Wasu daga cikin hanyoyin da aka sanya Fastocin sun hada da titin Murtala Muhammad, Airport Road, da Titin Sani Marshal a Kano.

Sauran titinun sun hada da titin Race Course, Bompai da wani yanki na titin gidan gwamnatin Kano.

Sannan babu wanda ya fadi wani abu kan bayyanar Fastocin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here