Jerin Wayoyin iphone da Android da Za su Dena Amfani da Manhajar WhatsApp

0
200

Akwai wayoyin Android da na iphone da dama da za su dena daukar manhajar WhatsApp daga farkon shekarar 2021.

Kamar yadda bayanai suka nuna daga sashin WhataApp FAQ, Manhajar za ta dinga aiki ne kadai a wayoyin da suke aiki kan version din 4.0.3 na Android da kuma na iOS 9 ko wadanda za’ayi fiye da su.

Dukkan wayoyin iphone 4 , za su dena amfani da WhatsApp a yan kwanaki kadan masu zuwa, wayoyin iphone din sun hada da iphone 4s, iphone 5, iphone 5S, iphone 6 da iphone 6S.

Wayoyin Android da za su dena amfani da WhatsApp sun hada da HTC, Motorola Droid Razr, LG Optimus Black da Samsung Galaxy S2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here