A watan Janairu Korona za ta Ƙara Munana a Najeriya – NCDC

0
330

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta yi gargadi ga ‘yan Najeriya cewa watan Janairu zai kasance mai muni ga ƙasar a ɓangaren yaduwar korona, yayin da suke ta fafutikar yaki da yaduwarta.

Darakta Janar na hukumar ta NCDC, Chike Ihekweazu wanda ya bayyana haka a yayin da yake jawabin da ya saba yi a kullum na kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona, ya ce ya yi wannan gargadin ne saboda mutane ba sa kiyaye dokokin da hukumomin lafiya da hadin guiwar gwamnatin Najeriya suka shimfida musu.

Wannan bayani daga Darakta Janar na hukumar ta NCDC na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ta shaida gagarumar yaduwar kwayar cutar.

Mista Ihekweazu ya kuma ce “mun fuskanci mako mafi muni tun bayan da muka fara yaki da yaduwar wannan annoba. Mun samu karin yaduwar cutar a Najeriya a makon jiya fiye da sauran makonnin tun bayan barkewar annobar.

“Hotuna da bidiyo daga fadin kasar na nuna halin abin bakin ciki da damuwa, saboda da alamu duk fadakarwar da muke yi, ko kuma kiraye-kirayen da muke yi wa ‘yan Najeriya a cikin watanni kadan da suka gabata, mutane ba sa kiyaye dokokin da aka shimfida, an cigaba da gudanar harkokin da aka saba yi a baya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “abin takaicin, watan Janairu zai kasance mai tsanani ga dukanninmu, wuraren da ake gudanar da bukukuwa da taruka na kara cika; cibiyoyin kiwon lafiyarmu sun cika sun batse; Muna ta faman shawo kam matsalar, muna ta faman neman yadda za mu kara wurare da kayan aiki, da suka hada da iskar shaka ta ‘oxygen don marasa lafiya.”

Ya kuma bayyana cewa a ko wane dare su kan amsa kiran wayoyi daga marasa lafiya da suka shigadamuwar a duba lafiyarsu inda ya ce al’amura za su kara muni, amma duk da haka sun samudamar yadda za su yi da abubuwan da suka kamata, ta hanyar hada guiwa dagwamnonin jihohi a fadin kasar don su aiwatar da matakan da dukanninsu suka amince a kai.

Shugaban hukumar ta NCDC ya kara da cewa sun gano cewa wasu jihohin sun fara daukar matakan na shawo kan cigaba da yaduwar kwayar cutar, amma kuma wasunsu sun yi wa batun rikon sakainar kashi ne kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here