2020: Jihar Jigawa Da Fitattun Mutanen Da Suka Rasu

0
153

 

Jihar Jigawa ta gamu da abubuwa na rashin daɗi, zulumi, jimami, fargaba, faɗiwar gaba, firgici, da alhini na faruwar abubuwa da dama wadda na tabbata jihar baza ta taɓa mantawa da wannan shekarar ba musamman da ta zama sanadin rasuwar manyan mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen cigaban jihar wasu aka dama dasu tun kafin samun ƴancin jihar, wasu sun sake fito da sunan jihar a idon duniya kama daga ma’aikatan gwamnati, ƴan siyasa, yana kasuwa, masu riƙe da sarauta da sauran al’umma.

Shekarar 2020, a jihar Jigawa za’a iya cewa ta shafi kowa kai tsaye ko ta wata fuska da ta shuka masa wani ciwo, alhini, ko firgicin da bazai manta dashi ba. Ɗauke uzurin Covid-19 da ta shafi dukkan duniya kuma ta taɓawa kowa uzurinsa ta tsayar da agogon duniya a tsaye chak.

Ita ce shekarar da aka rasa Rt. Hon. Adamu Ahmed Sarawa, tsohon kakakin majalisar dokokin jiha, Farfesa Haruna Wakili, tsohon kwamishinan Ilmi kuma mataimakin shugaban jami’ar Bayero, Rt. Hon. Ilyasu Sa’idu Dunduɓus tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa, Hon. Yahaya Muhammad Bigman tsohon ɗan majalisar dokoki mai wakiltar Sule Tankarkar, Hon. Adamu Fagen Gawo tsohon ɗan majalisar Garki da Ɓaɓura, Hon. Aminu Sidi Ƴalleman, tsohon kwamishinan jihar Jigawa, Alhaji Yusuf Alassan, Barman Gumel, Alhaji Haruna Idris Magama

Khadi Muhammad Inuwa Ali, tsohon Grand Khadi na jiha, Alhaji Sabo Ɗangƴatum, Hon. Aƙilu Liman Auyakayi tsohon shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Hon. Babangida Milo Hadejia, Dr. Abdulƙadir Isa Dutse tsohon shugaban asibitin Mallam Aminu Kano,

Alhaji Abubakar Abdullahi Sarkin Gabas Dutse/ King Maker, Hakimin Shuwarin, Alh Lawan Gwaram, Ɗan Darman/Council Member, Alhaji Ali Maitama Gwaram (Sarkin Shanun Dutse/Council Member, Alhaji Saleh Chiroma (Sarkin Fada Dutse/Council Member, Alhaji Bashir Aujara, Sarkin Yamma Dutse/ Hakimin Chamo

Alhaji Sabo Muhammed, Galadiman Gumel, Acting Senior Councillor & Council member, Alh Jibo Muhammed Council member representing traders, Alhaji Ayuba Muhammed Sarkin Kudu, Hakimin Meɗu, Alhaji Yusuf Alhassan, Barman Gumel, Alhaji Sani Ibrahim Magajin Garin Gumel Hakimim Gumel Kudu, Alhaji Idris Muhammed, Matawallen Gumel Council member, Alhaji Lawan Garba Falakin Gumel, Malam Ibrahim Albasu, Talban Gumel Malam Musa Adamu, Uban doman Gumel.

Maji daɗin Hadejia, Ɗan Malikin Hadejia Hakimin Waje, Haruna Idris Magama Kogunan Hdejia, Alhaji Isma’il Ibrahim, Jarman Ringim, Eng. Kamilu Umar Matawallen Ringim, Sanata Garba S. Taura, Sarkin Yaƙin Ringim da sauransu da dama.

Jihar tayi fama da sace – sace da asarar rayuka saboda sata daga ɓarayi, anyi garkuwa da al’umma da dama wasu an same su wasu sun rasa rayukansu sanadin haka, jihar tayi asarar rayuka da yawa sanadin hatsarin mota. Al’ummomi da dama a jihar nan sun rasa iyayensu, yayunsu, surukunsa, abokansu, da danginsu

Muna roƙon Allah kar ya maimaita mana irin wannan shekarar, Allah ya zaunar da jihar mu lafiya ya kawo mana arziƙi mai ɗorewa ya ɗaukaka al’ummarmu su shahara a fannon rayuwa kamar yadda suka shahara a lokacin mulkin Sule Lamido.

Mansur Ahmed
30/12/2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here