Ƴan Sanda sun Kama Waɗanda Su ka Shirya Baɗalar Nuna Tsiraici a Kaduna

0
200

Yan sanda sun kama shugabanin kungiyar wayward wadanda ake zargin suna da hannu a bayyana taron tsiraici da za’a yi a Kaduna.

Shagalin bikin na tsiraici, wanda matasa su ka dinga yadawa a shafukan sadarwa an shirya yinsa ne a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2020.

Wadanda su ka shirya bikin sun bukaci duk wadanda ke so halarta zai zo tsirara kuma zai zo da kwaroran roba don kariya.

Mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna kan kafafen yada labarai, Abdullah Yunus Abdallah a wata tattaunawa da BBC ya tabbatar da kama wadanda su ka shirya bikin.

“Lambar wayar wadanda suka shirya taron an sanyata a jikin takar gayyata wacce da ita aka yi amfani wajen gano su”, inji shi.

Wannan ne dai karo na farko da aka shirya taron tsiraici a arewacin Najeriya. Wanda hakan ya ja hankalin al’umma da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here