Zargin Luwaɗi Da Ɗan Shekara 11: An Dakatar Da Shugabar Makarantar Deeper Life da ke Akwai Ibom

0
252

Hukumomin makarantar Deeper Life sun dakatar da shugabar makarantar dake birnin Uyo, na jihar Akwa Ibom bisa zargin ɗaliban Makarantar da  yin luwadi da Ɗalibin  makarantar mai shekaru 11 mai suna Don Davies.

Dakatarwa ta biyo bayan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sadarwa na zamani wanda mahaifiyar yaran ta wallafa inda ta ke zargin daliban manyan aji a makarantar sun ci zarafin danta.

Yayin da aka tuntubi Misis Solomon Ndidi, shugabar makarantar ta tabbatar da cewa an dakatar da ita.

Ta kara da cewa, gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shiga lamarin, kuma ana kan bincike.

“Davies dalibi na ne bazan musanta ba. Abinda ya faru a makaranta abinda wanda yake waje bazai gane bane. Ana bincike kan lamarin yanzu haka saboda gwamnati ta shiga lamarin”, inji Ndidi.

” Bana son yin magana sosai akai saboda ana bincike na. Hukumomin makaranta sun dakatar dani. Don haka zan ci gaba da hakuri har sai gwamnati ta kammala bincikenta. Yan sanda da jami’an tsaron farin kaya suna cikin masu bincike”, inji fa.

A wani faifan bidiyo da yanzu haka ke yawo a shafukan sadarwa na zamani. Wata mata mai suna Deborah Okezieh ta ce dan ta mai shekaru 11, daliban makarantar sun yi lalata dashi sau dayawa.

Ta ce ta fahimci hakan ne yayin da ta nemi tattaunawa ta musamman da dan nata yayin ziyarar da ta kai makarantar.

“Yayin da na ganshi a wannan hali, na dauke shi zuwa mota, yana tsoro, ya ce idan ya yi magana za su kashe ahi”, inji Okezieh.

Ta ce ta nemi taimakon wani dalibi a makarantar don sanin abinda ke faruwa da danta.

” na yi magana da wani yaro wanda ya fada min cewa, an dauke shi daga JSS 1 zuwa SSS 1 yayin da yaje chan, dalibai a jin kwanan karatu suna amfani da hanaye da kafafuwa wajen shafa gabansa” inji matar.

Yaron ya ce “yayin da na isa wajen sai su cire min Wando”.

Davies ya kara da cewa, daliban su na fada masa cewa indai har ya fadawa shugabar makarantar ko mahaifiyarsa za su kashe shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here